Yadda zaka gano kowanne password da ka manta

 Yadda zaka gano kowanne password da ka manta


Idan ka manta Password ɗinka na wani Account da ka taɓa buɗewa zaka iya gano shi koda kuwa bakayi Forgot Password ba, musamman idan layin naka ya ɓata..

Sau tari layukan wayoyinmu sukan ɓata ko wayar ta ɓace gashi mun buɗe wani Account mai muhimmanci, ƙila Facebook ne ko wani Account na Social media wanda kuma mun manta password ɗin, gashi layin bayanan bare muyi Forgot Password su turo mana Code.

Zaka iya gano Password ɗin ta wata hanya mai sauƙi, amma sai idan ya kasance ka taɓa Saving Password ɗin ga Google, nasan kuna yawan ganin da zaran kun ƙirƙiri password na wata Application ko wani Plateform kamfanin Google yana baku damar kuyi saving na Password ɗin, to da zaran kunyi saving zai ajiye maku shi saboda irin hakan, yadda abun yake shine idan kana neman Password naka na ko wane kalan Account da ka taɓa buɗewa da wayarka to abinda zakayi shine kaje kai tsaye kashiga Setting na wayar bayan ya buɗe maka sai kashiga wurin da zakaga an rubuta "Google"



 bayan ya buÉ—e zai baka Options da yawa sai kaje wurin da aka rubuta "AutoFill" 



ka danna wurin, zai buÉ—e maka da Options guda ukku sai ka danna wurin da aka rubuta "AutoFill With Google" 



ka tabbatar kanada Gmail Account, bayan kayi hakan zai buÉ—e maka wani Page, zakaga wurin da aka rubuta Password sai kawai ka danna wurin, zai bayyanar maka da "Password CheckUp" a kasa zakaga duk wasu Website ko Plateform da ka taba buÉ—e masu Password, kana danna website É—aya a ciki zai buÉ—e maka da Username É—inka da Password naka duk zaka gani a wurin.


Ga Cikakken bayani nan a Hoton dake ƙasa.👇👇






Please share to your friends






Close Menu